14 Satumba 2024 - 07:20
Kungiyar Hizbullah Ta Sake Yi Ruwan Makamai Masu Linzami Kan Gwamnatin Sahyoniyawa

Majiyoyin labarai sun ba da rahoton cewa, an harba rokoki da dama a cikin yankunan da aka mamaye tare da kara kararrawa a yankuna daban-daban na sahyoniyawa.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya  nakalto maku daga Kamfanin dillancin labaran Irna shima bisa ya nakalto daga shafin sadarwa tashar Al-Mayadeen cewa, majiyoyin labarai sun bayyana cewa, an kai hari a arewacin yankunan da aka mamaye tare da kai hari kan wani muhimmin wuri na yahudawan sahyoniyawa a yankin Jalil.

Waɗannan majiyoyin sun jaddada cewa an yi ta jin ƙarar sautin kararrawar haɗari a yankin "Dufif" da ke Yammacin Jalil.

Wakilin Al-Mayadeen a Kudancin Lebanon ya kuma ruwaito cewa, an harba rokoki da dama zuwa yankin Al-Jalil da aka mamaye.

Kazalika majiyoyin yahudawan sahyoniya sun bayar da rahoton cewa, an ji karar kararrawa a wasu matsugunan yahudawan sahyoniya da ke yankin Gabar Jalil da Safed ciki har da Kahal.

A yayin da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta nuna goyon bayanta ga al'ummar Gaza da kuma gwagwarmayar Palastinawa, da kuma mayar da martani ga mamayar da gwamnatin sahyoniya ta ke yi a yankunan kudancin kasar da gidajen fararen hula, musamman a yankin Al-Ahmadiyeh, hedkwatar Falasdinu. Ta kai hari da makami mai linzami na Katyusha da dama matsuganan Arewacin Sahayoniya da sansanin Al-Jalil da ma'ajiyar kayan aikinta a yankin Ami’ad.

A wani labarin kuma, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Labanon ta sanar da cewa, ta hari wata tankar yaki Merkava na yahudawan sahyoniya wacce ke kan hanyar Ruisat Alam zuwa Zabedin da makami mai linzami.

A wannan harin dai an lalata tankar Merkava inda ta kama wuta.

Gwamnatin yahudawan sahyoniya wadda ta sha kaye a fagen daga da kungiyar Hizbullah, tana kai hare-hare kan wasu mazauna yankunan kudancin kasar Labanon da kuma kan iyakar kasar da Falasdinu da ta mamaye domin rama cin galabr da akai a kansu.

A ci gaba da wadannan hare-hare marasa manufa da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai kan mazauna yankunan kudancin kasar Labanon, mutane da dama ne suka yi shahada da kuma jikkata.

Domin mayar da martani ga wadannan hare-hare, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a kullum tana kai hare-hare kan sansanonin yahudawan sahyoniya da matsugunai daban-daban da makamai masu linzami da jirage marasa matuka.